ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

INEC Na Nazarin Sauya Jadawalin Zaɓen 2027 Da Ya Faɗo A Watan Azumi

by Abubakar Sulaiman
7 months ago
INEC

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Hukumar INEC ta ce tana nazarin yiwuwar duba jadawalin babban zaɓen 2027 bayan koke-koken da suka taso kan daidaituwar ranar 20 ga Fabrairu, 2027 da watan azumin Ramadan. Tun da farko, hukumar ta ayyana cewa za a gudanar da zaɓen Shugaban Ƙasa da na Majalisar Tarayya a ranar 20 ga Fabrairu, yayin da na gwamnoni da majalisun jihohi za su gudana a ranar 6 ga Maris, 2027.

Wasu ’yan ƙasa, musamman Musulmi, sun nuna damuwa cewa zaɓe a lokacin azumi na iya shafar fitowar masu kaɗa ƙuri’a da aikin jami’an zaɓe. Cikin masu kira da a sake duba ranar akwai tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, wanda ya ce ranar ta faɗo daidai cikin Ramadan (7 Fabrairu zuwa 8 Maris, 2027). Tsohon hadimin shugaban ƙasa, Bashir Ahmad, shi ma ya buƙaci a sake tunani domin tabbatar da cikakkiyar halartar jama’a.

  • Rikicin Cikin Gida Na Jam’iyyun Siyasa Na Yin Mummunan Tasiri Ga Sahihancin Zaben Nijeriya – INEC
  • Shehu Sani Ya Yi Allah-Wadai Da Buƙatar Shugaban INEC Ya Sauka

Sai dai INEC, ta bakin Kwamishinan Yaɗa Labarai da Ilimantar da Masu Zaɓe, Mohammed Haruna, ta ce jadawalin ya yi daidai da Kundin Tsarin Mulki na 1999 (da aka yi wa kwaskwarima), Dokar Zaɓe ta 2022 da ƙa’idojin gudanar da zaɓe da suka tanadi cewa zaɓen shugaban ƙasa da na majalisar tarayya su gudana a Asabar ta uku na watan Fabrairu a shekarar zaɓe.

ADVERTISEMENT

Duk da haka, hukumar ta ce tana sauraron damuwar masu ruwa da tsaki, kuma za ta ci gaba da tuntuɓar ɓangarori daban-daban, tare da yiwuwar neman matakin majalisa idan ya zama dole, domin duk wani sauyi ya kasance cikin iyakar doka. INEC ta jaddada aniyarta na gudanar da zaɓe cikin gaskiya, da haɗin kai da sahihanci.

INEC
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Next Post
Taki

Dalilin Gwamnatin Tarayya Na Samar Da Kundin Amfani Da Takin Zamani

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.