ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Majalisar Dokokin Kano Ta Kafa Kwamitin Tantance Garo A Matsayin Mataimakin Gwamna

by Abubakar Sulaiman
5 months ago

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta tabbatar da karɓar wasiƙar Gwamna Abba Kabir Yusuf wadda ke neman tantance Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamna. Kakakin majalisar, Jibrin Ismaila Falgore, ne ya sanar da hakan bayan karanta wasiƙar a zaman majalisa ranar Laraba.

Wannan na zuwa ne bayan naɗin da gwamnan ya yi wa Garo domin cike gurbin da ya samu sakamakon murabus ɗin Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo a watan da ya gabata. A cikin wasiƙar, gwamnan ya bayyana halayen kirki, da kwarewa da gogewar Garo, tare da irin gudunmawar da ya bayar ga jam’iyyar APC da kuma ci gaban jihar Kano.

Naɗin ya yi daidai da sashi na 191(3) na Kundin Tsarin Mulki na 1999 (wanda aka gyara), wanda ke bai wa gwamna damar naɗa mataimaki idan gurbi ya samu. Bayan karanta wasiƙar, kakakin majalisar ya sanar da kafa kwamitin wucin gadi domin tantance wanda aka naɗa.

ADVERTISEMENT

Kwamitin, ƙarƙashin jagorancin mataimakin kakakin majalisa, ya kunshi manyan shugabannin majalisa da wakilan mazaɓu daban-daban, kuma ana sa ran zai gayyaci Garo domin tantancewa tare da miƙa rahotonsa ga majalisar ranar Litinin.

Garo mai shekaru 48 ya riƙe mukamai da dama a baya, ciki har da shugaban ƙaramar hukuma, da shugaban ALGON Kano, da kwamishina da kuma ɗan takarar mataimakin gwamna na APC a zaɓen 2023.

LABARAI MASU NASABA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote
  • Abubakar Sulaiman
    Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa

MASU ALAKA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna
Siyasa

Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna

September 9, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Next Post
An Kaddamar Da Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Fannin Kasuwanci Na Sin Da Afirka A Kasar Habasha

An Kaddamar Da Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Fannin Kasuwanci Na Sin Da Afirka A Kasar Habasha

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

September 10, 2026
Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

September 10, 2026
Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.