ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tashar Jiragen Ruwa Ta Lekki Ta Fara Tarbar Kwantaina Daga Kasashen Afirka

by Leadership Hausa
8 months ago
lekki

Daga Abubakar Abba

Tasahar Jiragen Ruwa ta Lekki da ke a Jihar Legas, ta fara tarbar manyan kayan da aka yo jigilarsu daga yankunan Tashoshin Jiragen Ruwa na wasu kasashen da ke Afirka, inda ta fara tarbar Kwantainoni kaso 20, da aka yo jigilaru a 2025.

Jaridar BusinessDay ta ruwaito cewa, hakan ya zama wata babbar nasara ta farko ga kasar nan, tun bayan fara gudanar da tura ababen hawa daga Tashar TinCan island a 2024. Zuwa kasar China.

  • Shari’ar Annabi SAW Ta Fi Ta Sauran Annabawa Sauƙi
  • Buƙatar A Sake Duba Sabuwar Dokar Haraji

A cewar wasu alkaluman da aka fitar a hukumance, a yanzu wajen ajiya kayan da aka yo jigilarsu a Tasahar, sun kai kimanin kaso 50 daga kaso 20, a watan Yulin 2025.

ADVERTISEMENT

Babban Jami’in da ke kula da ke sanya ido a wajen da akae ajiya kaya a Tasahar ta Lekki Ajay Tyagi, ya bayyana cewa, a yanzu haka ana sauke Kwantainoni da dama a wajen aje kayan na Tashar wadanda kuma ake tura su zuwa Tashar Jiragen Ruwa ta Tema, da ke a kasar Côte d’Iboire.

Tyagi ya sanar da cewa, Tashar ta Lekki, na ci gaba da samun karuwar shigo da Kwantainoni kafin kaisu, zuwa wasu kasuwannin da ke makwabtaka da da sauran kasashe.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Taron Bikin Maulidi Ya Gudana A Unguwar Mile 12 A Legas

NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba

Shi kuwa Manajan Darakta da ke kula da wajen aje kayan a Tashar ta Lekki Jedrzej Mierzewski, ya sanar da cewa, kasuwar ta cikin kasar nan na kara bayar da wata damar wajen janyo ra’ayin masu shigo da kaya ta ruwa, zuwa cikin kasar nan.

Ya kara da cewa, hakan na kuma kara samar da sauki wajen shigo da kaya ta hanyar ruwa, zuwa cikin kasar.

Mierzewski ya kuma yi gargadi da cewa, tura kayan ya danganta ne, bisa yin hadin guiwa a tsakanin masu tafiyar da wguraren da ake ajiye kayan da aka shigo da su da masu sanya ido da kuma abokan hudda.

“Muna bukatar mu rinka yin aiki kafada da kafada da sauran masu ruwa da tsaki da ke a fannin na sufurin Jiragen Ruwa, kuma zamu iya samar da farashin da za a iya yin gasa akansa wanda ya yi daidai da tsarin sufurin Jiragen Ruwa na kasar nan, “Inji shi.

Ya yi nuni da cewa, yanayin kwarewar da aka samu daga kasar Poland ta shekaru da dama, wani misali ne kan yadda hakan ya samar da sabon babin gudanar da gasa a Tashar Jiragen Ruwan.

A cewarsa, a wancan lokacin daga Tashar Jiragen Ruwan ta kasar ta Poland, ana tura kaya zuwa Tashoshin Jiragen Ruwa na kasar Jamus

A cewar mahukuntan Tashar ta Lekki, a yanzu haka ana sauke mayan motoci kimanin 200 da suka yo jigilar kaya zuwa Tashar, wanda hakan ke ci gaba da faruwa, saboda samar da na’urar zamani da a turance, ake kira da electronic call-up system wacce ke kara ingnata ayyukan da ake gudanarwa a Tashar.

Kazalika, mahukuntan Tashar sun bayyana cewa, kara fadada aikin Tashar ta Lekki, ya dogara ne kawai kan kara samun gudanar da ayyuka tare da kara samar da kayan aiki a daukacin tsarin na hada-hadar sufurin Jiragen Ruwa.

Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?
  • Leadership Hausa
    An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu
  • Leadership Hausa
    Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja
  • Leadership Hausa
    Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

MASU ALAKA

Yadda Taron Bikin Maulidi Ya Gudana A Unguwar Mile 12 A Legas
Tattalin Arziki

Yadda Taron Bikin Maulidi Ya Gudana A Unguwar Mile 12 A Legas

September 4, 2026
NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
Tattalin Arziki

NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba

September 4, 2026
NPA Ta Tabbatar Da Maido Da Manyan Kayan Aikin Hukumar Wuta Ta Neja Delta —Babbar Manaja
Tattalin Arziki

NPA Ta Tabbatar Da Maido Da Manyan Kayan Aikin Hukumar Wuta Ta Neja Delta —Babbar Manaja

August 28, 2026
Next Post
Gwamna Abba Ya Kammala Shirye-shiryen Komawa APC A Ranar Litinin

Gwamna Abba Ya Kammala Shirye-shiryen Komawa APC A Ranar Litinin

LABARAI MASU NASABA

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

September 10, 2026
Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.