ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, July 7, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsayuwa Da Kafa Biyu Ya Fi Tsayuwa Da Kafa Daya

by Rabi'u Ali Indabawa
4 months ago
Tsayuwa

Lokacin da na karbi ragamar aiki a matsayin Ministan Tsaro, na yi alawarin karfafa tsarin tsaron kasar. Na jaddada cewa, da farko, a matsayinmu na ‘yan Nijeriya dole ne mu dauki alhakin daukar nauyin da kalubalen da kasarmu ke fuskanta.

Wannan ba kawai magana ba ce, illa kira ne zuwa aiki. Ina kuma tsaye daram wajen tabbatar da cewa mun fuskanci kalubalen tsaronmu kai tsaye ta hanyar amfani da falsafar “hadin kai da manufa daya”, wadda ke nufin mu yi aiki tare a matsayin kungiya guda, maimakon kowanne bangare ya yi aiki shi kadai kamar rundunar da ke zaman kanta.”

  • Sarkin Musulmi Ya Bukaci A Sauya Fasalin Tsarin Tsaro A Yaki Da Ta’addanci
  • Rawar Da Sashen Ayyukan Hidimomi Da Biyan Bukatu Ke Kara Takawa A Kasar Sin 

“Wannan ita ce falsafar da na bi a duk tsawon aikina na hidimta wa kasa a mukaman jagoranci da na ma’aikata a cikin aikin sojin Nijeriya. Wannan tunani ya ci gaba da kasancewa tare da ni har zuwa yau.

Na kuma saba da bai wa jami’ai kwarin gwiwa da ke karkashina su fahimci muhimmancin wannan tunanin na dabarun tsaro, tare da aiwatar da shi a duk inda suka tsinci kansu a cikin aikinsu.

Matsayin da nake rike da shi a yau yana da nufin karfafa tsarin tsaron kasar, bisa ga umarnin da Bola Ahmed Tinubu, Babban Kwamandan Askarawan Nijeriya, ya ba ni.

Ina da cikakken kuduri da himma wajen mayar da fata da burin ‘yan Nijeriya su zama gaskiya ta hanyar kawo karshen ta’addanci a kasar.”

Daidaitawar Soji Da Farar Hula

“A lokacin da nake hidima a matsayin jami’in soja, daya daga cikin kalubalen da na fuskanta shi ne daidaita tunanin soja da al’adun farar hula. Akwai lokuta da dama da dole ne mutum ya saurari ra’ayin farar hula wajen magance matsalolin tsaro yayin da suke faruwa.

A lokutan da na bi ra’ayin farar hula, na ga sakamakon da na samu a matsayin kwamanda ya burge ni matuka. Duk da na san cewa wasu daga cikin shawarar da na yanke ba su yi wa wasu daga cikin sojojina dadi ba, amma a matsayina na kwamanda, dole ne su amince da hukuncin da na yanke.

A koyaushe ni nake daukar alhakin wadannan shawarwari. Idan na waiwaya baya yanzu, ina farin ciki da na yanke wadannan matakai domin sun tabbatar da cewa suna da amfani sosai.”

Haramtaccen Yaki Da Ingantacce

Yakin da bai da daidaito ba za a auna shi da yawan ‘yan ta’adda da aka kashe a daji kawai ba, amma da yawa akwai mutanen da aka ‘yanto daga shiga ta’addanci ko aka fito da su daga daji. Wannan yana nuna juriya a yaki, wato daga kirga gawarwaki zuwa halastaccen mulki.

Yakin da ‘yan ta’adda ke yi yana da wahala kuma sau da yawa yana taba yunkurin dakaru ne kawai, wanda hakan zai kai ga jama’a su gaji da jinkirin samun sakamako. Amma halattaccen yaki yana mai da hankali kan gano tushen matsalolin da ke haddasa rikicin. Saboda haka, dabarun aikina sun ginu ne a kan hada wadannan hanyoyi biyu domin samun sakamako mai dorewa.

Nadin da aka yi min daga baya a matsayin Babban Hafsan Tsaro (CDS) ya ba ni damar fadada gano abin da ake kira “Tsarin Borno” a cikin ayyukan soji.

Ina tuna cewa a lokacin da nake CDS, a taron Kwamandojin Rundunar Hadin Gwiwa na CDS mai taken Inganta hadin Kai A Sansanin Soji”, na jaddada muhimmancin hadin kai wajen aiki, amfani da dabaru, da kuma hada al’umma baki daya wajen magance matsalolin tsaro.

Misali, canza sunan aikin hadin gwiwar soja a Jihar Filato daga ‘Operation Safe Haben’ zuwa ‘Operation Enduring Peace’ wanda an yi shi ne domin samar da sabon hangen nesa ga sojoji da al’ummomin yankin kan muhimmancin yin aiki tare domin samar da zaman lafiya mai dorewa a Jihar Filato.

Ina alfahari da cewa wannan dabarar tana aiki a jihar da kuma a sauran wuraren da sojojin Nijeriya ke gudanar da ayyukansu a fadin kasar.

Dabarun Hada Kan Al’umma

Akwai wani abu da na fahimta wanda nake son jaddadawa. Ba kasafai ake ganin sa a fili a cikin al’umma. A halin yanzu muna yaki ne da rikici mai sassa da dama. Kungiyoyin ta’addanci kamar Boko Haram, ISWAP, da Lakurawa da wasu kungiyoyin masu tashin hankali sun hada kai, sun ajiye sabanin da ke tsakaninsu domin su yi aiki tare su kai hare-hare. A wasu lokuta ma suna musayar bayanan sirri a tsakaninsu.

Wannan gaskiya ce, kuma shi ya sa ake bukatar abin da ake kira “tsayuwa da kafafu biyu”, wato hada dabarun karfi na soja da kuma dabarun da ba na soja ba a cikin ayyukan tsaronmu, domin samar da daidaito da ake bukata wajen kayar da ta’addanci.

Idan kungiyoyin ta’addanci na iya hada kai, me zai hana jama’ar kasa su hada kai da sojoji? Ba za mu iya kayar da ta’addanci da bindigogi da harsasai kawai ba. Wannan shi ne ainihin sakon da nake son isarwa a wannan rubutu.

Kwarewata a matsayin Kwamandan Yanki da Babban Hafsan Tsaro har yanzu tana da tasiri sosai a tunanina. Na kalli matsalolin daga matsayi na jagoranci da na ma’aikata. Misali, yanke shawarar bin ra’ayin farar hula ta hanyar yin hadin kai ba tare da tangarda ba da gwamnatin Jihar Borno ya haifar da gagarumar nasara a yaki da ta’addancin Boko Haram.

Wannan kuma yana karfafa hujjata ta cewa tsaro nauyi ne da kowa ke dauka. Wannan shi ne tsarin aiki a kasashen da suka ci gaba. Ban yarda cewa tsarinmu ya kamata ya bambanta ba.

Wannan shi ne tsarin da Ma’aikatar Tsaro ke aiwatarwa. Ina farin cikin ganin cewa dukkan sassan sojojin Nijeriya sun daidaita da wannan dabarar. Haka kuma ma’aikatar tana yin hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki a cikin al’umma, cibiyoyin addini da na gargajiya, kafofin yada labarai, kungiyoyin farar hula, da sassan kasuwanci na musamman domin shiga cikin dabarar “Hadin Kan Al’umma Gaba daya” wajen magance kalubalen tsaro na kasa.

Mun tsara wani samfurin aika sako wanda ya dace da kowane matsayi na al’umma, har ma da mazauna karkara. Manufar ita ce samar da wayar da kai cewa idan muka hada kai, za mu iya kai da ta’addanci kasa idan muka dage a kan hakan.

Akwai abubuwa da dama da ke haifar da rashin tsaro, amma akwai hanya daya da za ta iya dakatar da shi. Kuma wannan hanya ita ce lokacin da ’yan Nijeriya suka dauki nauyin hakan, ba tare da la’akari da al’adu ko kabila ba. Wannan nauyi ne na tilas domin juya yanayi a kan wadanda ba sa fatan alheri ga kasarmu.

‘Yan Kallo Da Ba Sa Kawo Dauki

Kwanan nan na gabatar da jawabi na musamman a taron shekara-shekara na Kungiyar Tsoffin Daliban Kwalejin Tarayya ta Kaduna a matakin duniya. Na jaddada cewa:

“Tarihi yana koya mana cewa babu wata kasa da za ta kasance mai tsaro idan ’yan kasarta suna zama masu kallo  da ba sa shiga tsakani.”

ADVERTISEMENT

Na ba da misali cewa manomi a Sakkwato, mai kasuwanci a Legas, da malami a Enugu suna zama layin farko na tsaro a kasa. Wannan yana kama da motsa muhawara kan tsaro daga sansanonin soja zuwa tituna, yana nuna cewa tsaro nauyi ne da ke wuyan kowa. Sojoji ba za su iya kasancewa a ko’ina ba. Saboda haka, ya zama dole ’yan Nijeriya su kasance masu shiga tsakani cikin tsarin tsaro, ba masu kallo marasa shiga tsakani ba.

Wannan rubutu na zaba masa take mai sauki wato “Tsayuwa da kafafu biyu ya fi tsayuwa da kafa daya”. Wannan dabara ce da ta dace da sabon tunani da muke kokarin gabatarwa.

LABARAI MASU NASABA

Matsalar Tsaro: Masana Sun Firgita Da Fitowar Sabon Bidiyon Bello Turji

Yadda Rikice-rikice Ke Ƙara Ta’azzara Talauci A Arewacin Nijeriya —Rahoto

Ina son sakon ya kai ga kowa, daga mai POS a Ibadan, mai dinki a Kaduna, har zuwa ma’aikacin gwamnati a Port Harcourt. Wannan wajibi ne, kuma yana dauke da alkawari zuwa ga ’yan Nijeriya na “tsayuwa da kafafu biyu” a yaki da ta’addanci.

Na dauki wannan alkawari ne a ranar 21 ga Satumba, 1991, lokacin da aka ba ni Kwamishinan Shugaban Kasa don aiki a Rundunar Sojan Nijeriya a matsayin jami’in soja  na kasa. Dole ne mu hada kai don canza al’adar tsaro ta kasa.

Tsayuwa
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Adadin Mutanen Da Tsananin Zafi Ya Kashe A Turai Ya Haura Dubu 1,300 —WHO
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Pakistan Ta Kashe Mutum 36 A Hare-haren Da Ta Kai Kan Iyakarta Da Afghanistan
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Dalilanta Na Sake Fasalin Hukumar NYSC
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Sarkin Zazzau Ya Umarci A Soke Wasu Al’adu Da Ke Kawo Wa Aure Cikas

MASU ALAKA

Matsalar Tsaro: Masana Sun Firgita Da Fitowar Sabon Bidiyon Bello Turji
Rahotonni

Matsalar Tsaro: Masana Sun Firgita Da Fitowar Sabon Bidiyon Bello Turji

June 26, 2026
An Kashe Mutane Da Dama Da Kone Gidajensu A Wani Hari Da Aka Kai Benuwai
Rahotonni

Yadda Rikice-rikice Ke Ƙara Ta’azzara Talauci A Arewacin Nijeriya —Rahoto

June 26, 2026
Noma
Rahotonni

Ƙa’idojin Gudanar Da Biyan Kuɗi Nan Take Domin Kare Kai Daga Zamba

June 26, 2026
Next Post
Kuncin Rayuwa: Jam’iyyun Adawa Da Kungiyar Kwadago Sun Caccaki Tinubu

Kuncin Rayuwa: Jam’iyyun Adawa Da Kungiyar Kwadago Sun Caccaki Tinubu

LABARAI MASU NASABA

Kasuwa Ce Ke Saita Tsarin Cinikayyar Sin Da EU In Ji Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin

Kasuwa Ce Ke Saita Tsarin Cinikayyar Sin Da EU In Ji Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin

July 6, 2026
Dukkan Kabilun Kasar Sin Na Zaman Tsintsiya Madaurinki Daya

Dukkan Kabilun Kasar Sin Na Zaman Tsintsiya Madaurinki Daya

July 6, 2026
Mutane 15 Sun Mutu A Hatsarin Mota A Jihar Kwara

Mutane 15 Sun Mutu A Hatsarin Mota A Jihar Kwara

July 6, 2026
Gwamnatin Sin Ta Fara Aika Zagayen Farko Na Kayakin Agajin Gaggawa Ga Venezuela

Gwamnatin Sin Ta Fara Aika Zagayen Farko Na Kayakin Agajin Gaggawa Ga Venezuela

July 6, 2026
FIFA Ta Tsallake Iyakarta Dangane Da Batun Dakatarwar Balogun – UEFA

FIFA Ta Tsallake Iyakarta Dangane Da Batun Dakatarwar Balogun – UEFA

July 6, 2026
Shugabannin Sin Da Madagascar Sun Yi Musayar Sakon Taya Murnar Cika Shekaru 20 Da Kulla Alakar Diflomasiyya Tsakaninsu

Shugabannin Sin Da Madagascar Sun Yi Musayar Sakon Taya Murnar Cika Shekaru 20 Da Kulla Alakar Diflomasiyya Tsakaninsu

July 6, 2026
Rashin Tsaro: Kisa Ne Ya Fi Cancanta Ga ‘Yan Ta’adda Ba Gyaran Hali Ba – Ɗan Majalisa Gagdi

Rashin Tsaro: Kisa Ne Ya Fi Cancanta Ga ‘Yan Ta’adda Ba Gyaran Hali Ba – Ɗan Majalisa Gagdi

July 6, 2026
Mu Leka Yadda Kasar Sin Ke Raya Hakkin Dan Adam Daga Taron Gefe Na UNHRC

Mu Leka Yadda Kasar Sin Ke Raya Hakkin Dan Adam Daga Taron Gefe Na UNHRC

July 6, 2026
ADC Ta Rushe Shugabannin Jam’iyyar A Kano, Ta Naɗa Kwamitin Riƙo

ADC Ta Rushe Shugabannin Jam’iyyar A Kano, Ta Naɗa Kwamitin Riƙo

July 6, 2026
Rundunar Sojin Ruwan Sin Ta Yi Gwajin Makami Mai Linzami Ta Amfani Da Jirgin Ruwa Mai Nutso

Rundunar Sojin Ruwan Sin Ta Yi Gwajin Makami Mai Linzami Ta Amfani Da Jirgin Ruwa Mai Nutso

July 6, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.