ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Muka Kashe Masu Garkuwa 4 Da Suke Shirin Kai Hari Kan Attajirai A Legas —CP

by Abubakar Sulaiman
3 months ago

Rundunar Ƴansanda ta Jihar Legas ta bayyana yadda jami’anta suka daƙile yunƙurin garkuwa da mutane tare da kashe wasu da ake zargi ƴan bindiga huɗu a wata arangama da ta faru a yankin Ejigbo.

Kwamishinan ƴansandan Jihar, Tijani Fatai, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar rundunar da ke Ikeja.

Ya ce lamarin ya faru ne a ranar 24 ga Mayu, 2026, da misalin ƙarfe 9:30 na dare, bayan samun sahihan bayanan sirri kan shirin yin garkuwa da wani ɗan kasuwa a ƙofar Jakande Estate da ke yankin Ejigbo.

ADVERTISEMENT

CP Fatai ya ce ƴan bindigar suna cikin wata shahararriyar ƙungiya da ke kai hari kan attajirai da ƴan kasuwa masu kuɗi a duk lokacin da suka shiga Jihar Legas domin aikata laifi.

Ya ƙara da cewa bincike ya nuna cewa shugaban ƙungiyar, wanda aka fi sani da Ifeanyi ko “Ifeko”, ya horar da wani Henry Asoona, wanda shi ma ake zargin jagoran wata ƙungiyar garkuwa da attajirai da aka taɓa murƙushewa a kasuwar Ladipo a shekarar 2024.

LABARAI MASU NASABA

NDLEA Ta Cafke Ƴar Shekara 67 Da Hodar Iblis Da Aka Ɓoye A Cikin Ayaba

Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’

A cewarsa, Ifeanyi yana zaune a ƙasashen waje amma ya dawo Legas domin tsara wannan aikin garkuwa da mutane.

Ya ce da suka hango ƴansanda, ƴan bindigar suka buɗe wuta, inda aka shiga musayar wuta mai zafi tsakaninsu da jami’an tsaro.

“Jami’anmu sun mayar da martani da ƙarfi, wanda ya kai ga hallaka mutum huɗu daga cikin su, yayin da ɗaya ya tsere da raunin harbi,” in ji shi.

Rundunar ta ce an kuma gano kayayyaki da dama daga wurin, ciki har da mota ƙirar Toyota Sienna, bindiga AK-47 guda ɗaya da harsashi 25, bindiga SMG da harsashi 12, da kuma makullan motoci ƙirar Toyota Corolla da Leɗus.

CP ɗin ya ƙara da cewa wani jami’in ƴansanda ya samu rauni a ƙafa yayin musayar wutar, kuma yana karɓar magani a asibiti.

Ya ce bincike na ci gaba domin kamo wanda ya tsere da sauran abokan aikinsu.

Haka kuma ya bayyana cewa rundunar ta kama wasu mutum 10 a cikin watan Mayu saboda laifuka daban-daban, tare da ƙwato makamai da abubuwa masu haɗari.

A ƙarshe, ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da amfani da bayanan sirri da dabarun aiki domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a faɗin Jihar Legas.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Tsaro

NDLEA Ta Cafke Ƴar Shekara 67 Da Hodar Iblis Da Aka Ɓoye A Cikin Ayaba

July 11, 2026
Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’
Tsaro

Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’

July 9, 2026
Sojoji Sun Kama Mai Kai Wa Ƴan Ta’adda Kayan Aiki A Zamfara
Tsaro

Sojoji Sun Kama Mai Kai Wa Ƴan Ta’adda Kayan Aiki A Zamfara

June 25, 2026
Next Post
Sin: A Sa Kaimi Ga Yunkurin Tabbatar Da Kwanciyar Hankali A Duniya

Sin: A Sa Kaimi Ga Yunkurin Tabbatar Da Kwanciyar Hankali A Duniya

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.