ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, June 5, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jam’iyyun Adawa Na Ƙara Matsa Ƙaimin Haɗin Gwiwa Don Kawar Da APC A 2027

by Abubakar Sulaiman
2 months ago

Biyo bayan rikice-rikicen shugabanci da ke girgiza jam’iyyun adawa a ƙasar nan, wasu daga cikin jam’iyyun adawa suna aiki a bayan fage don gabatar da haɗin gwiwa wajen kawar da jam’iyyar APC a garagar mulki a 2027.

Jam’iyyar ADC kwanan nan ta fuskanci rikicin shugabanci, lokacin da tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar, Nafiu Bala Gombe, ya nemi kotu ta bayyana shi a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa.

2027: Batun Murabus Din Masu Rike Da Mukaman Gwamnati

ADVERTISEMENT

2027: Guguwar Buƙatar Neman Tsige Shugaban INEC Na Ƙara Zafafa

Bala wanda ya ƙi tsarin da ya kai ga haifuwar da shugabancin Sanata Daɓid Mark, ya ƙaryata cewa ya ajiye muƙaminsa da niyya zama mamba a kwamitin gudanarwa na ƙasa na jam’iyyar.

LABARAI MASU NASABA

’Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice Daga APC Zuwa ADC da PRP

‘Yan Majalisar Wakilai 6 Daga Oyo Sun Fice Daga PDP Zuwa APM

Tsarin ya kai ga matakin rikici lokacin da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta soke kwamitin gudanarwa na jam’iyyar da Daɓid Mark ke jagoranta.

Kafin yanzu, babban jam’iyyar adawa ta PDP wacce ta shiga rikici tun bara an raba ta gida biyu, tare da wani rukunin mai biyayya ga gwamnonin jam’iyyar da Kabiru Tanimu Turaki ke jagoranta da kuma wani rukuni mai biyayya ga ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, wanda Abdulrahman Mohammed ke jagoranta.

Duk da haka, bayan rikicin da ya faru a ADC, yawancin jam’iyyun adawa sun haɗa kai da shugabanninsu, inda wasu majiyoyi ke cewa wata sabuwar haɗin gwiwa na iya fitowa domin ƙalubalantar APC mai mulki.

A wani taro tsakanin ADC da ɓangaren PDP da Turaki ke jagoranta, Gwamnan Jihar Oyo Seyi Makinde ya ce taron na nuna goyon baya ne ga ADC, amma mai magana da yawun ɓangaren Ini Ememobong ya shaida wa ƴan jarida cewa har yanzu taron zai ci gaba.

Haka kuma a cikin wani rubutu bayan taron, Turaki ya bayyana cewa taron wani ɓangare ne na ƙoƙarin tsayawa don kare ƙa’idodin dimokuraɗiyya waɗanda suka wuce iyakar jam’iyya.

Ya kuma ce akwai yarjejeniya cewa dole ne a kiyaye dimokuraɗiyya, ka da a yi shiru kuma dole ne a a kare haƙƙin ƴan adawa.

An ruwaito cewa a cikin ƴan kwanaki masu zuwa, akwai yiwuwar ƙarin jam’iyyun adawa su haɗu tare da ADC don fuskantar APC.

Amma yayin da yake magana da ƴan jarida bayan taro da ADC a ƙarshen mako, shugaban jam’iyayar PRP, Dakta Hakeem Baba-Ahmed ya ce ziyarar Mark tana da nufin nuna ta’aziyya ga jam’iyya kan abin da ke faruwa a kwanakin baya da kuma “Rashin jin dadinmu kan abin da ya bayyana a matsayin shiga cikin muhimman cibiyoyin gwamnati a harkokin jam’iyyu na siyasa.”

Ya ce PRP ba sa farin ciki game da abin da ake ganin tsoma bakin a cikin tsarin dimokuraɗiyya kuma ziyarar ta kasance don tabbatar wa ADC cewa PRP wacce aka kafa bisa ƙa’idodin dimokuraɗiyya, adalci da gaskiya za ta goyi bayan kowace jam’iyya, ba kawai ADC ba kowace jam’iyya da ake ganin tana fama da farmaki, wanda ba a yi adalci ba, kawai siyasa wanda zai haifar da matsaloli ga tsarin dimokuraɗiyya a ƙasar nan.

Ya ce, “Mu jam’iyya ce da ke da imani da adalci da gaskiya, wannan dimokuraɗiyya ce mai jam’iyyu da dama, dole ne ta yi aiki a matsayin dimokuraɗiyya mai jam’iyyu da dama. Muna son a gudanar da zaɓe mai cike da ƴanci da gaskiya a shekarar 2027. Ba za mu iya samun sahihin zaɓe mai cike da gaskiya ba a shekarar 2027, idan jami’an gwamnati ta yi katsalandan a harkokin jam’iyyu. Muna cikin damuwa sabada abin da yake faruwa ga ADC na iya faruwa ga sauran jam’iyyu.

“Mun gama taronmu na ƙarshe, muna godiya ga Allah cewa ba mu bai wa kowa dama ko yanayi da zai sa mu samu rauni ba. Lokacin da muke ganin abin da ke faruwa da jam’iyyun siyasa kamar ADC, ba za mu iya barci cikin kwanciyar hankali ba. Za mu ci gaba da aiki, domin a shekarar 2027, mu iya ba ƴan Nijeriya zaɓi kuma da ikon Allah za mu yi hakan.

“A cikin wannan yanayin, muna buƙatar a cire dukkan takunkumi da aka sanya ga ADC da sauran jam’iyyun adawa.”

Yayin da yake magana kan kawance, Dakta Hakeem ya ce akwai kawance a fili, amma jam’iyyu kaɗan ne ke shirin miƙa wuya.

Ya ƙara da cewa, “Muna son tsarin da yake bayyane. Idan ADC ta karya dokokin ƙasa, ko ta yi wa wani ɓangare na kundin tsarin mulki ko dokoki abin da bai dace ba, muna sa ran a yi musu hukunci bisa yadda doka ta tanada. Muna sa ran a yi musu shari’a mai cike da adalci.

“Ba za mu ce kar jam’iyyun siyasa su bi dokokin ƙasa ba, amma abin da za mu ce shi ne, tsoma baki a harkokin siyasa a wajen waɗannan dokoki na ƙasa ba za a lamunci hakan ba, kuma za mu yi adawa da su.

“Muna da yaƙinin cewa sauran jam’iyyun adawa za su haɗa kai da mu domi yaƙar abin da ke faruwa ba daidai ba. Za mu tsaya tare da ADC a kan wannan batu. Za mu goyi bayansu ta kowace hanya da muka iya kuma da fatan sauran jam’iyyun za su zo haɗa kai da mu.

“Hukumar shari’armu tana tare da mu, yana da matuƙar muhimmanci hukumar shari’a ka da ta nuna kamar tana aiki ne domin amfanin gwamnati. Muna gaya wa ƴan Nijeriya ka da su yanke tsammani saboda tabbas za mu yi gwagwarmaya don wannan.”

Game da zargin da ake yi wa INEC, ya ce, “A kowanne lokaci ya kamata INEC ta kasance mai gaskiya, domin tana da matuƙar muhimmanci wajen mulkin dimokuraɗiyya. INEC ba hukuma ba ce ta kare jam’iyya mai mulki. Hukuma ce da ya kamata ta gudanar da kanta a matsayin mai adalci. A wannan mataki, abin da za mu iya faɗi shi ne, INEC tana nuna kamar tana ɗaya daga cikin jam’iyyun a zaɓe kuma ba haka bane. Tana gudanar da zaɓuka kuma za ta iya gudanar da ingantattun zaɓuka ne kawai idan ta bar kowa ya yi aiki cikin iyakokin aikinsa da dokokinsa.”

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴansanda Sun Daƙile Yunƙurin Garkuwa Da Wasu Ma’aurata A Abuja
  • Abubakar Sulaiman
    Sabon Rikicin Manoma Da Makiyaya yayi Ajalin Mutuwar Mutane 7 A Bauchi
  • Abubakar Sulaiman
    Hajji 2026: Mahajjata 1,905 Sun Dawo Nijeriya Daga Saudiyya
  • Abubakar Sulaiman
    Matatar Dangote Ta Ƙara Yawan Man Da Take Tacewa Zuwa Ganga 700,000

MASU ALAKA

Majalisa Ta Nemi Tinubu Ya Canza Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci Don Kawo Ƙarshen Kashe-kashe
Siyasa

’Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice Daga APC Zuwa ADC da PRP

June 3, 2026
‘Yan Majalisar Wakilai 6 Daga Oyo Sun Fice Daga PDP Zuwa APM
Siyasa

‘Yan Majalisar Wakilai 6 Daga Oyo Sun Fice Daga PDP Zuwa APM

June 3, 2026
Gwamnatina Za Ta Mayar Da Hankali Kan Buƙatun Al’ummar Nasarawa – Wadada
Siyasa

Gwamnatina Za Ta Mayar Da Hankali Kan Buƙatun Al’ummar Nasarawa – Wadada

June 1, 2026
Next Post
Tinubu Ya Sanya Hannu Kan Kasafin 2026 Na Naira Tiriliyan 68.32, Ya Tsawaita Ayyukan 2025

Ƴan Majalisar Wakilan ADC Sun Buƙaci A Gurfanar Da Shugaban INEC A Kotu

Discussion about this post

LABARAI MASU NASABA

Ma’aikatar Kasuwanci Ta Sin: Za a Gudanar Da Bukukuwa Fiye Da 100 Na “Fitar Da Kayayyaki Zuwa Kasar Sin” a Shekara Ta 2026

Ma’aikatar Kasuwanci Ta Sin: Za a Gudanar Da Bukukuwa Fiye Da 100 Na “Fitar Da Kayayyaki Zuwa Kasar Sin” a Shekara Ta 2026

June 5, 2026
Xi Jinping Zai Kai Ziyarar Aiki A DPRK

Xi Jinping Zai Kai Ziyarar Aiki A DPRK

June 5, 2026
Bukatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

Bukatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

June 5, 2026
‘Symbolic Interactionism’:Sabuwar Makaranta A Kimiyyar Zamantakewa

‘Symbolic Interactionism’:Sabuwar Makaranta A Kimiyyar Zamantakewa

June 5, 2026
An Cafke Motocin Dako 50 Makare Da Abinci Za Su Shiga Nijar A Zamfara

Shekara 3 Da Shirin Ceto Jihar Zamfara: Jinjina Ta Musamman Ga Gwamna Dauda Lawal

June 5, 2026
Jami’an Tsaro Sun Cafke Masu Garkuwa Da Mutane 4, Sun Ceto Uwa Da Ɗanta A Bauchi

Jami’an Tsaro Sun Cafke Masu Garkuwa Da Mutane 4, Sun Ceto Uwa Da Ɗanta A Bauchi

June 5, 2026
An Yi Tir Da ‘Yan Takarar Da Suka Fice Daga APC Saboda Faduwa Zabe

An Yi Tir Da ‘Yan Takarar Da Suka Fice Daga APC Saboda Faduwa Zabe

June 5, 2026
Ƴansanda Sun Daƙile Yunƙurin Garkuwa Da Wasu Ma’aurata A Abuja

Ƴansanda Sun Daƙile Yunƙurin Garkuwa Da Wasu Ma’aurata A Abuja

June 5, 2026
Kotu Ta Yi Gwanjon Kaddarorin Sani Sha’aban Bisa Taurin Bashi

Kotu Ta Yi Gwanjon Kaddarorin Sani Sha’aban Bisa Taurin Bashi

June 5, 2026
An Yi Suka Kan Mayar Da Nijeriya Jujin Jibge Kwantaina Da Ake Shigowa Da Su

An Yi Suka Kan Mayar Da Nijeriya Jujin Jibge Kwantaina Da Ake Shigowa Da Su

June 5, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.